Wata Amarya ta cinye kazar Amarci kafin ango ya gama sallar nafila .
Kamar dai yanda kuka sani al'adar mu ta hausawa idan namiji yayi sabon aure to abokai sayi kayan lallashin Amarya irin su ; gasashshiyar kaza , Lemun roba da sauran kayan makulashe domin su raka shi dakin Amarya .
To haka shima wannan angon ta faru dashi , bayan abokai sun tafi sai ango yayi alwala domin gabatar da sallar nafila yayin da ya bar Amarya cikin daki .